Hausa Insights

BASIRAR AIKI DA YAREN HAUSA

  • Maraba da zuwa shafin karin haske akan yadda zaka rubuta baitin waka

kokuma fassara baitin waka tare da Musixmatch, a wannan shafin zaka samu

karin haske sosai a kan abunda kake nema idan ma baka gane wani abu ba,

kokuma babu abunda kake nema a nan, kana iya garzayawa ka nemi taimako

a wajen yan uwa abokan aiki.

  • Gane amfanin wakilin suna a Hausa da yadda ya kamata ayi amfani da su a wajen rubutu

A cikin yaren hausa, akwai abunda ake kira da “Wakilin Suna”, shi wakilin suna

ya kunshi kalmomi irin su ‘’Shi,” ‘’Ita”, ‘’Su”, ‘’Mu”, ‘’Ni”, da kuma‘’Ke”, yana da

amfani kowa ya san cewa dukka wadannan kalmomi suna zaman kan su ne

kuma ba a hade su wajen rubuta kalma, Idan har aka hade su hakan na iya

kawo matsala ta rashin bada ma’ana mai kyau, kokuma ma bada wata

ma’anar chan daban, kuma indai har akayi haka baza a samu sakon da ake

bukatar samu ba.


Domin karin bayani ga misalai nan:

Wakilin Suna (Pronoun) Yadda mutane suka cika amfani dasu ❌ Misalin amfani da su yadda ya kamata ✅
Ba Ba’a magana a nan Ba a magana a nan
Ita Itace ta sace mani waya Ita ce ta sace mani/mini waya
Ya Yayi karatu Ya yi karatu

A layi na farko na wannan teburi, zaku ga kalma ta ‘’Ba’’ tana zaman kanta ne.

Dalili shine kalmar ‘’a’’ din dake karshe a kalmar ‘’Ba a’’ tana zaman kanta ne

domin baki ce kalmar ‘’a’’ din dake karshe


Ku tuna cewa, bakaken harshen Hausa sune: A," "I," "O," "U," da kuma "E."

  • Gane yadda ake amfani da wasu kalmomi masu wakafi na sama (’)

Yadda ake amfani dasu ba dai-dai ba ❌

Yadda suke a dai-dai 

A a A’a
Addu a Addu’a
Alada Al’ada
Alajabi Al’ajabi
Alaura Al’aura
Al umma Al’umma
Arba in Arba’in
Baaskare Ba’askare
Bala i Bala’i
Bidi a Bidi’a
Casain Casa’in
Daawa Da’awa
Da ira Da’ira
Du ai Du’a’i
Da a Da’a
Dabi a Dabi’a
Faida Fa’ida
Fara a Fara’a
Fi ili Fi’ili
Jami a Jami’a
Jima i Jima’i
Juma a Juma;’a
Hani an Hani’an
ya yan Ya’yan
Sha awa Sha’awa
Sa a Sa’a

Ya (Na mace)

yar

‘ya

‘yar

Yan ‘yan
Ya ya (Na ‘yan yara) ‘ya ya

Wadannan misalai sune suke karin bayani a kan yadda ake amfanin da su ba dai-dai ba da kuma yadda ya kamata ace suke a ka’ida.

  • Kalmomi da aka cika samun matsala wajen rubuta su da yadda ya kamata a rubuta su

Yadda ake rubuta su ba dai-dai ba ❌ Yadda ya kamata a ce ana rubuta su ✅ Misalin amfani dasu yadda ya kamata✅
Bayti Baiti Zaiyi maku baiti mai dadi
Can Chan A chan gurin na baro ta
Canza Chanza Miya faru ne duk kin chanza?
Hanun Hannun Sai naga hannun ma duk kanta
Kauna Kauna Ke nake kauna
Kaye Kayi Kayi rawa kai malam
Kece a zuciya ta Kece a zuciya ta Kece a zuciya ta
Pakewa Fakewa Miyesa kai baka daabun fakewa?
Qalbi Kalbi Ka sanya ni a kalbi
Qallabi Kallabi Wannan kalabi na ne
Qauna Kauna Ke nake kauna
Qwarjini Kwarjini Kayi kwarjini
Raiza Reza Bani reza ta
Soya Suya (ta nama) Ina za a samu mai suya?
Taqi Taki Taki daukar wayar
Tohm Toh Toh naji zancen ka
Tsapta Tsafta Ina neman mace mai tsafta
Tunon Tonan Bazan taba tonan asiri ba
Vava Baba Baba ina kwana

Yana da amfani kowa ya gane cewa harshen Hausa baya amfani da wadanan bakake P, Q da kuma V a wajen rubutu. Wadanan bakake ba a amfani dasu wajen hada kalma a Hausa kuma babu su a Hausa gabakidaya, sabida haka idan za a rubuta baiti kokuma fassara baiti tare da Musixmatch ba a yadda ayi amfani da su ba.


P. Q da kuma V - ❌


  • Duk wata kalma kokuma baiti na wani yare a barshi a yadda yazo kar a chanja shi ayi kokarin maida shi rubutun Hausa.
  • Yadda za ayi amfani da kalmomi idan an mai-maita su tare da sa masu karen-dori ‘’(-)” a tsakanin su, ga misalai nan
Yadda mutane suka cika amfani dasu ❌ Yadda ya kamata ace ana amfani dasu ✅ Misalin amfani da su yadda ya kamata ✅

Ah ah

Ah, ah

Ah-ah


Na ce, “Ah-ah hattara yarinya”

Dai dai

Dai, dai

Dai-dai Dolle inyi komai dai-dai

Shishshigi

Shish shigi

Shish, shigi

Shish-shigi Ita din ta cika shish-shigi
  • Yadda ake rubuta abunda wani ya fada ta hanyar rubuta abinda ya fada a cikin (‘’) kuma kafin asa alamar a kan rufe da alamar dakatawa (,) kamar yadda akayi bayani a tsare-tsaren rubuta baiti na Musixmatch, Kuma harafin farko na abinda ake fada za a rubuta shi ne da babban baki. Akwai misali da yayi karin bayani a kan haka
Yadda mutane suka cika amfani dasu ❌ Yadda ya kamata ace ana amfani dasu ✅ Misalin amfani da su yadda ya kamata ✅

Tache

Sukache

Yache

Niche


Ta ce

Suka ce

Ya ce

Na ce

Ta ce, “Kai ne a raina”

Suka ce, “Soyayya ruwan zuma

Ya ce, “Ki bani dama”


  • Karin bayani akan kalmomin da aka ara daga Larabchi

Maganar farko kuma maganar dake a kan gaba, muna so mu nuna cewa bamu karya wata doka ba akan tsare-tsaren rubuta baiti na Musixmatch wadda take fadar ‘’Ya zama dolle a rubuta kowace kalma da asalin rubutu” , Kuma daga bangaren mu muna nuna goyon baya akan haka sabida yin amfani da hakan na nuna cewa ana a’dana al’ada ta kowane yare, siyasa muka ga yana da amfani mu kara haske a kan wannan bangaren domin nan gaba

Dagaske ne yaren Hausa, da ake yi sosai a tsakanin kasashen Africa, ya aro wasu kalmomi daga harshen larabchi daga tarihi. Wadannan kalmomi yawancin su ana fadar su ne kamar yadda ake fadi a harshen larabchi, kuma ma wasu ma’anar tasu daya, babu banbanci sai dai yadda ake rubuta su daban a harshen Hausa dukda cewa akwai wa’anda ana rubuta su ne kamar yadda ake rubuta na harshen larabchi.

  • Ga misalai nan domin karin bayani:

Native (Hausa)

Romanized (Arabic) ❌ Native (Arabic)❌ Meaning in Arabic Meaning in Hausa
Abada 'Abadan أَبَدًا Never/Forever Forever
Alama Ealama عَلَامَة Sign Sign
Alhamdulillahi Alhamd lillh اَلْحَمْدُ لِلَّهِ‎ Praise be to God/ Thank God Praise be to God/ Thank God
Baiti Bayt بَيْت House/Verse Verse
Barka Baraka بَرَكَة Grace/Good Form of greeting (Good)
Bala'i Bala' بَلَاء Disaster Disaster
Casa'in Tisewun تِسْعِين 90 Numbers ninety in Hausa
Daraja Daraja دَرَجَة Degree Worth, fame and value
Dalili Dalil دَلِيل Proof Reason or proof
Duniya Dunya دُنْيَا World World
Fa'ida Fayida فَائِدَة Benefit Importance of doing something
Fara'a Farha فَرْحَة Happiness To be always happy
Fitila Fatila فَتِيلَة‎ Fuse Light
Gadara Ghudara غَضَارَة Abundance Arrogant or Pride
Gafara Ghufar غَفْر Forgive or Excuse Used as greetings (mostly women) And also means excuse me
Ganima Ghanima غَنِيمَة‎ Loot Anything that is obtained illegally/Maybe goods or money.
Hadari Khatar خَطَر Danger Accident or Danger
Hankali Eaql عَقْل Quick-witted Someone with good sense
Hidima Khidma خِدْمَة Service Services

Idan aka duba wannan misalali sun dan yi bayani a kan irin kalmomi da ake magana an same su daga harshen larabawa

Gasu nan da yadda ake rubuta su da kuma ma’anar su.

Akan wannan bangaren idan akwai abun da mutum bai gane ba ko yake kokonto, toh ya garzaya ya nemi taimako daga cikin abokan aiki masu gane harshen Hausa.

Did this answer your question? Thanks for the feedback There was a problem submitting your feedback. Please try again later.