BASIRAR AIKI DA YAREN HAUSA ✏️
Maraba da zuwa shafin karin haske akan yadda zaka rubuta baitin waka
kokuma fassara baitin waka tare da Musixmatch, a wannan shafin zaka samu
karin haske sosai a kan abunda kake nema idan ma baka gane wani abu ba,
kokuma babu abunda kake nema a nan, kana iya garzayawa ka nemi taimako
a wajen yan uwa abokan aiki.
Gane amfanin wakilin suna a Hausa da yadda ya kamata ayi amfani da su a wajen rubutu
A cikin yaren hausa, akwai abunda ake kira da “Wakilin Suna”, shi wakilin suna
ya kunshi kalmomi irin su ‘’Shi,” ‘’Ita”, ‘’Su”, ‘’Mu”, ‘’Ni”, da kuma‘’Ke”, yana da
amfani kowa ya san cewa dukka wadannan kalmomi suna zaman kan su ne
kuma ba a hade su wajen rubuta kalma, Idan har aka hade su hakan na iya
kawo matsala ta rashin bada ma’ana mai kyau, kokuma ma bada wata
ma’anar chan daban, kuma indai har akayi haka baza a samu sakon da ake
bukatar samu ba.
Domin karin bayani ga misalai nan:
Wakilin Suna (Pronoun) | Yadda mutane suka cika amfani dasu ❌ | Misalin amfani da su yadda ya kamata ✅ |
Ba | Ba’a magana a nan | Ba a magana a nan |
Ita | Itace ta sace mani waya | Ita ce ta sace mani/mini waya |
Ya | Yayi karatu | Ya yi karatu |
A layi na farko na wannan teburi, zaku ga kalma ta ‘’Ba’’ tana zaman kanta ne.
Dalili shine kalmar ‘’a’’ din dake karshe a kalmar ‘’Ba a’’ tana zaman kanta ne
domin baki ce kalmar ‘’a’’ din dake karshe
Ku tuna cewa, bakaken harshen Hausa sune: A," "I," "O," "U," da kuma "E."
Gane yadda ake amfani da wasu kalmomi masu wakafi na sama (’)
Yadda ake amfani dasu ba dai-dai ba ❌ | Yadda suke a dai-dai ✅ |
A a | A’a |
Addu a | Addu’a |
Alada | Al’ada |
Alajabi | Al’ajabi |
Alaura | Al’aura |
Al umma | Al’umma |
Arba in | Arba’in |
Baaskare | Ba’askare |
Bala i | Bala’i |
Bidi a | Bidi’a |
Casain | Casa’in |
Daawa | Da’awa |
Da ira | Da’ira |
Du ai | Du’a’i |
Da a | Da’a |
Dabi a | Dabi’a |
Faida | Fa’ida |
Fara a | Fara’a |
Fi ili | Fi’ili |
Jami a | Jami’a |
Jima i | Jima’i |
Juma a | Juma;’a |
Hani an | Hani’an |
ya yan | Ya’yan |
Sha awa | Sha’awa |
Sa a | Sa’a |
Ya (Na mace) yar | ‘ya ‘yar |
Yan | ‘yan |
Ya ya (Na ‘yan yara) | ‘ya ya |
Wadannan misalai sune suke karin bayani a kan yadda ake amfanin da su ba dai-dai ba da kuma yadda ya kamata ace suke a ka’ida.
Kalmomi da aka cika samun matsala wajen rubuta su da yadda ya kamata a rubuta su
Yadda ake rubuta su ba dai-dai ba ❌ | Yadda ya kamata a ce ana rubuta su ✅ | Misalin amfani dasu yadda ya kamata✅ |
Bayti | Baiti | Zaiyi maku baiti mai dadi |
Can | Chan | A chan gurin na baro ta |
Canza | Chanza | Miya faru ne duk kin chanza? |
Hanun | Hannun | Sai naga hannun ma duk kanta |
Kauna | Kauna | Ke nake kauna |
Kaye | Kayi | Kayi rawa kai malam |
Kece a zuciya ta | Kece a zuciya ta | Kece a zuciya ta |
Pakewa | Fakewa | Miyesa kai baka daabun fakewa? |
Qalbi | Kalbi | Ka sanya ni a kalbi |
Qallabi | Kallabi | Wannan kalabi na ne |
Qauna | Kauna | Ke nake kauna |
Qwarjini | Kwarjini | Kayi kwarjini |
Raiza | Reza | Bani reza ta |
Soya | Suya (ta nama) | Ina za a samu mai suya? |
Taqi | Taki | Taki daukar wayar |
Tohm | Toh | Toh naji zancen ka |
Tsapta | Tsafta | Ina neman mace mai tsafta |
Tunon | Tonan | Bazan taba tonan asiri ba |
Vava | Baba | Baba ina kwana |
Yana da amfani kowa ya gane cewa harshen Hausa baya amfani da wadanan bakake P, Q da kuma V a wajen rubutu. Wadanan bakake ba a amfani dasu wajen hada kalma a Hausa kuma babu su a Hausa gabakidaya, sabida haka idan za a rubuta baiti kokuma fassara baiti tare da Musixmatch ba a yadda ayi amfani da su ba.
P. Q da kuma V - ❌
Duk wata kalma kokuma baiti na wani yare a barshi a yadda yazo kar a chanja shi ayi kokarin maida shi rubutun Hausa.
Yadda za ayi amfani da kalmomi idan an mai-maita su tare da sa masu karen-dori ‘’(-)” a tsakanin su, ga misalai nan
Yadda mutane suka cika amfani dasu ❌ | Yadda ya kamata ace ana amfani dasu ✅ | Misalin amfani da su yadda ya kamata ✅ |
Ah ah Ah, ah | Ah-ah
| Na ce, “Ah-ah hattara yarinya” |
Dai dai Dai, dai | Dai-dai | Dolle inyi komai dai-dai |
Shishshigi Shish shigi Shish, shigi | Shish-shigi | Ita din ta cika shish-shigi |
Yadda ake rubuta abunda wani ya fada ta hanyar rubuta abinda ya fada a cikin (‘’) kuma kafin asa alamar a kan rufe da alamar dakatawa (,) kamar yadda akayi bayani a tsare-tsaren rubuta baiti na Musixmatch, Kuma harafin farko na abinda ake fada za a rubuta shi ne da babban baki. Akwai misali da yayi karin bayani a kan haka
Yadda mutane suka cika amfani dasu ❌ | Yadda ya kamata ace ana amfani dasu ✅ | Misalin amfani da su yadda ya kamata ✅ |
Tache Sukache Yache Niche
| Ta ce Suka ce Ya ce Na ce | Ta ce, “Kai ne a raina” Suka ce, “Soyayya ruwan zuma Ya ce, “Ki bani dama”
|
Karin bayani akan kalmomin da aka ara daga Larabchi
Maganar farko kuma maganar dake a kan gaba, muna so mu nuna cewa bamu karya wata doka ba akan tsare-tsaren rubuta baiti na Musixmatch wadda take fadar ‘’Ya zama dolle a rubuta kowace kalma da asalin rubutu” , Kuma daga bangaren mu muna nuna goyon baya akan haka sabida yin amfani da hakan na nuna cewa ana a’dana al’ada ta kowane yare, siyasa muka ga yana da amfani mu kara haske a kan wannan bangaren domin nan gaba
Dagaske ne yaren Hausa, da ake yi sosai a tsakanin kasashen Africa, ya aro wasu kalmomi daga harshen larabchi daga tarihi. Wadannan kalmomi yawancin su ana fadar su ne kamar yadda ake fadi a harshen larabchi, kuma ma wasu ma’anar tasu daya, babu banbanci sai dai yadda ake rubuta su daban a harshen Hausa dukda cewa akwai wa’anda ana rubuta su ne kamar yadda ake rubuta na harshen larabchi.
Ga misalai nan domin karin bayani:
Native (Hausa) ✅ | Romanized (Arabic) ❌ | Native (Arabic)❌ | Meaning in Arabic | Meaning in Hausa |
Abada | 'Abadan | أَبَدًا | Never/Forever | Forever |
Alama | Ealama | عَلَامَة | Sign | Sign |
Alhamdulillahi | Alhamd lillh | اَلْحَمْدُ لِلَّهِ | Praise be to God/ Thank God | Praise be to God/ Thank God |
Baiti | Bayt | بَيْت | House/Verse | Verse |
Barka | Baraka | بَرَكَة | Grace/Good | Form of greeting (Good) |
Bala'i | Bala' | بَلَاء | Disaster | Disaster |
Casa'in | Tisewun | تِسْعِين | 90 | Numbers ninety in Hausa |
Daraja | Daraja | دَرَجَة | Degree | Worth, fame and value |
Dalili | Dalil | دَلِيل | Proof | Reason or proof |
Duniya | Dunya | دُنْيَا | World | World |
Fa'ida | Fayida | فَائِدَة | Benefit | Importance of doing something |
Fara'a | Farha | فَرْحَة | Happiness | To be always happy |
Fitila | Fatila | فَتِيلَة | Fuse | Light |
Gadara | Ghudara | غَضَارَة | Abundance | Arrogant or Pride |
Gafara | Ghufar | غَفْر | Forgive or Excuse | Used as greetings (mostly women) And also means excuse me |
Ganima | Ghanima | غَنِيمَة | Loot | Anything that is obtained illegally/Maybe goods or money. |
Hadari | Khatar | خَطَر | Danger | Accident or Danger |
Hankali | Eaql | عَقْل | Quick-witted | Someone with good sense |
Hidima | Khidma | خِدْمَة | Service | Services |
Idan aka duba wannan misalali sun dan yi bayani a kan irin kalmomi da ake magana an same su daga harshen larabawa
Gasu nan da yadda ake rubuta su da kuma ma’anar su.
Akan wannan bangaren idan akwai abun da mutum bai gane ba ko yake kokonto, toh ya garzaya ya nemi taimako daga cikin abokan aiki masu gane harshen Hausa.